An yi jana'izar Galadiman Kano

Hakkin mallakar hoto

An gudanar da sallar jana'izar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim, wanda ya rasu a tsakar daren Lahadi a babban birnin Nigeriar Abuja.

Dubban jama'a ne suka halarci jana'izar ta Galadiman na Kano ciki har da mataimkain shugaban Nigeria Arc. Muhammad Namadi Sambo.

Marigayi Galadiman Kano wanda babban dan majalisar sarkin Kano ne, na da karfin fada a ji a masarautar Kano.