Microsoft ya kaddamar da Xbox One

Hakkin mallakar hoto
Image caption A yanzu, wasanni goma ne aka sanya a cikin sabon Xbox, amma za a kara yawansu nan gaba

Kamfanin Microsoft ya kaddamar da sayar da wasannin bidiyo na Xbox One a China.

Hakan ya sa kamfani ya zama na farko daya shigo cikin wannan harka mai tsoka ta sayar da wasannin bidiyo.

An sayar da na'urar wasannin bidiyon na farko ne akan kudi dala 699 a birnin Shanghai.

Kawo yanzu dai kamfanin Sony da Nintendo ba su kaddamar da sayar da na su wasannin bidiyo na Xbox ba.

A watan Janairu daya gabata gwamnatin kasar China ta dage haramcin sayar da wasannin kumfuta na kasashen waje da aka kwashe shekaru 14 ana yi saboda fargaba akan abubuwan da ke kunshe a wasannin.

Sai dai za'a so ke wasu fitattun wasanni da suka hada da wasan nan mai taken 'Call of Duty' a wasannin bidiyon.

Kawo yanzu dai wasanni 10 ne kadai ke cikin Xbox One, sai dai Microsoft ya ce akwai wasu wasanni kusan 70 da ke tafe.

Tun da farko a shirya kaddamar da Xbox One ne a makon daya gabata, sai dai aka jinkirta yin hakan, kuma Microsoft bai bayyana dalilin da ya sa aka samu jinkirin ba.

Yanzu haka dai ana binciken kamfanin na Amurka bisa zargin keta wasu dokokin mallakar fasaha.