Rahoton Bankin Duniya game da kasuwanci a Nigeria

Bankin duniya ya kaddamar da wani sabon rahoto a kan hanyoyin bunkasa zuba jari da kafa masana'antu a Nijeriya.

Rahoton wanda aka gabatar a ranar Litinin din nan cikin birnin Abuja na da lakabin "Gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya a shekara ta 2014."

Karo na uku kenan da bankin duniyar ke kaddamar da irin wannan rahoto bayan nazarin ka'idojin kafa masana'antu a fadin kasar.

Binciken na bankin duniya wani bangare ne na shirye-shiryen da kasar ke yi don farfado da kanana da matsakaitan masana'antu da nufin yaki da talauci.

Bankin Duniya ya ce an samu bunkasar harkokin zuba jari da masana'antu a Nijeriya. Ya ce jihohin kasar 22 sun gudanar da bincike a kan hanyoyin bunkasa kafa masana'antu a kasar, ko da yake akwai bukatar su kara kwazo.