An lafta wa wani dan wasan zari-ruga tara

Hakkin mallakar hoto NFL
Image caption Ba a san takamaimai a kan me aka ci tarar dan wasan ba, yin sulu, sujada ko addu'ar da ya yi

Hukumar kula da kwallon zari-ruga ta Amurka ta ci wani dan wasa musulmi tara saboda yin sujada a lokacin da yake murnar cin kwallo.

Dan wasan kungiyar Kansas City Chiefs, Husain Abdullah ya yi sulu ya gurfana a kan gwiwoyinsa sannan ya sa goshinsa a kasa bayan ya ci kwallo a lokacin wasansu da New England Patriots.

Abun da dan wasan ya yi ya saba da dokokin Hukumar na yin murnar da ta wuce gona da iri bayan cin kwallo.

Sai dai masu suka sun ce akwai son kai a hukuncin Hukumar kwallon zari-rugar, don kuwa 'yan wasa kiristoci da dama na murna ta hanyar alamta addininsu idan sun ci kwallo, amma ba a hukunta su.