Magoya bayan Hama sun nuna rashin gamsuwa

Image caption Hama Amadou ya ce ya bar Nijar ne saboda barazanar da ake yi wa rayuwarsa

Magoya bayan shugaban majalisar dokokin jamhuriyar Nijar Mallam Hama Amadu sun ce ba su gamsu da sammacin da wata babbar kotun Niamey ta bayar don kama shi ba.

Magoya bayan Hama Amadou sun ce kamata ya yi kotu ta ba da sammaci na kasa da kasa ganin cewa mutumin da ake neman kamawar na kasashen waje ne amma ba Nijar ba.

Tun da farko, hukumomi sun ba da sammacin kama shugaban majalisar dokokin kasar, wanda ya fice zuwa kasar Faransa, bayan an zarge shi da safarar jarirai.

Sai dai bangaren gwamnatin na ganin kalaman magoya bayan shugaban majalisar dokokin tamkar katsalandan ne cikin ayyukan kotu.