Amnesty ta nemi yi wa wata 'yar Iran rai

Hakkin mallakar hoto amnesty
Image caption Amnesty ta ce matashiyar ta ce ba ita ce ta kashe mutumin ba, ko da yake ta amsa haka da bakinta

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta duniya Amnesty International ta bukaci Iran kada ta zartar da hukuncin kisa ga wata Matashiya da aka same ta da laifin kashe wani mutum, wanda ta ce ya yi kokarin cin zarafinta.

Rahotanni daga Iran sun nuna cewa ana iya rataye matashiyar, Reyhaneh Jabbari wadda shekarunta 26 a Talatar nan.

Kungiyar Amnesty ta ce an zartar mata da hukuncin kisa ne, bayan gudanar da wani bincike mai cike da kura-kurai.

An kama Reyhaneh Jabbari ne a shekara ta 2007, bisa zargin kashe wani tsohon jami'in ma'aikatar leken asiri na kasar.