Isra'ila ta ce Iran tafi IS hadari

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr. Netanyahu ya ce idan Iran ta mallaki makamin kare dangi, zata fitini duniya

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kasar Iran a matsayin wata babbar barazana ga kasashen duniya fiye da mayakan IS masu da'awar kafa daular musulunci.

A jawabin sa a taron Majalisar Dinkin Duniya, Mr Netanyahu ya ce bai kamata a kyale Iran ta ta rika sarrafa nukiliya ba, domin za ta iya kera makaman kare dangi.

Sai dai jakadan Iran a majalisar Dinkin Duniya, Javad Safaei, ya ce wadannan kalamai basu cancanta ba, inda ya ce Isra'ila tayi kaurin suna wajen tara muggan makamai da suka hada da makaman kare dangi.

Mr. Safaei ya ce Isra'ila da tayi kaurin suna a aikata manyan laifuka, da kowa ya sani harda majalisar dinkin duniya, bai kamata ta samu bakin zargin wasu kasashe ba.