An lakadawa Raila Odinga duka

An lakadawa jagoran 'yan adawa na kasar Kenya Mr Raila Odinga duka da tsumagiya, lokacin wani taron gangamin siyasa.

Mr Odinga wanda tsohon Pira minista ne, an yi ta zabga masa bulalar ne bayan da ya fara tikar rawa da wasu mata a taron gangamin.

Mutumin da ya lakada masa dukan ya ce ya ga Mr Odinga na matsawa kusa da matarsa ne lokacin da yake tsakiyar cashe rawar.

Wasu rahotanni sun ce wannan ya sa ayar tambaya kan ko mahukunta sun samarwa da jagoran 'yan adawar kariyar da ta kamata.

Bayan da suka sake mutumin da yayiwa Mr Odinga bulalar , jami'an tsaro sun ce me yiwuwa yana fama da tabin hankali ne.