Yara goma sun sake kamuwa da shan inna

Hakkin mallakar hoto
Image caption An gano sabbin wadanda suka kamun ne lokacin da cibiyar kula da ci gaban da aka samu wajen yaki da polio ke ganawa a London

An tabbatar da gano yara goma da suka kamu da cutar shan inna a baya-bayan nan a kasar Pakistan, adadi kusan mafi yawa da aka samu a cikin shekaru goma.

Ya zuwa yanzu akwai yara 184 da ke dauke da cutar shan inna a Pakistan.

Akasarin sabbin yaran da aka gano dauke da shan inna a kasar yankunan kabilu ne da ke arewa maso yamma na Pakistan.

Pakistan na daya daga cikin kasashe uku kacal da suka hadar da Nijeriya da Indiya da ke fama da annobar cutar shan inna a duniya.

A karkashin sabbin tanade-tanaden da aka bullo da su a farkon wannan shekara, jazaman duk dan Pakistan ya samu shaidar yi masa allurar riga-kafin shan inna kafin ya fita zuwa kasashen ketare.