Shafin Snapchat na fuskantar kutse

Image caption Saboda matsalar kutse, ana aikawa masu amfani da Snapchat tallace-tallacen shafukan rage kiba

Shafukan sada zumuntan mutane da yawa a shafin Snapchat, sun fuskanci matsalar kutse, al'amarin da ya sa suke aikawa da sakonnin da ba ayi niyyar aikasu ba.

Sai dai shafin na Snapchat ya ce bai gamu da wata matsala ta kutse ba.

Kutsen, ya sa ana amfani da bayanan mutanen da ke amfani da shafukan sada zumunci na Snapchat, inda ake aikawa da tallace-tallacen wasu shafuka na masu aikin ragewa mutane kiba.

Babu masaniya ko mutane nawa ne matsalar ta shafa, amma masu amfani da shanfin Snapchat a wasu kasashe masu yawa sun ta yin korafi a shafin Twitter akan wannan matsala.

Shafin Snapchat ya gamu da matsaloli na karya ka'idojin aiki a baya, wadanda suka hada da bari a san sunaye da lambobin wayar mutane miliyan hudu da dubu dari shida da ke amfani da shafin a watan Janairu.

A wancan lokaci, wani shafin intanet mai suna, SnapchatDB ya bayyana sunaye da lambobin masu amfani da shafin Snapchat, sai dai SnapchatDB bai bayyana sauran lambobi biyun karshen lambobin ba.

Masu tafiyar da shafin na SnapchatDB su ka ace sun yi hakan ne domin su nuna irin barakar da shafin sada zumunci na Snapchat bai gyara ba.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masana al'amuran tsaron intanet sun ce Snapchat ya je baya ta fuskar tsaro

A wata sanarwa, shafin Snapchat ya ce matsalar da aka samu ta kwana-kwanan nan saboda an samu bayanan mutanen ne a wasu shafukan intanet.

''Mun ga sheda da ke nuna cewa masu kutse sun saci bayanan mutane daga wasu shafukan intanet, kuma sun fara amfani da bayanan domin samun shiga shafukansu na Snapchat'', Shafin Snapchat ya shaida wa BBC.

''A wasu lokuta da dama, muna sanarda masu amfani da shafinmu cewa sun samu matsala da shafukansu''.

''Mu na ba masu amfani da shafin mu shawara su rika amfani da bayanan sirri masu sarkakiya na bada damar shiga shafukansu''.

Shafin Snapchat wanda aka kaddamar a 2011, ya fuskanci matsaloli na tsaron shafukan mutane da suke amfani da shi.

An tsara manhajar Snapchat ce ta yadda za a rika aikawa da hotuna da sakonni masu saurin bacewa. Amma an kirkiri wata manhajar mai suna Snapchat Hack wadda ke bada damar a adana sako na tsawon lokaci.

Wani mai bincike kan tsaro a intanet, Brian Honan ya ce shafin Snapchat ya ja baya ta fuskar tsaro, kuma hakan zai iya korar masu amfani da shi.