Rabin Namun dajin duniya ya kare –Bincike

Masu kare Namun daji sun bayyana damuwa game da ayyukan masu fasa-kwaurin hauren giwa

Asalin hoton, Environmental Foundation Ltd

Bayanan hoto,

Masu kare Namun daji sun bayyana damuwa game da ayyukan masu fasa-kwaurin hauren giwa

Wani sabon bincike ya yi gargadin cewa adadin namun daji a fadin duniya ya ragu da fiye da rabi a cikin shekaru arba'in.

Wata kungiya mai rajin alkinta namun daji, Worldwide Fund Nature ta ce asarar da aka yi ta dabbobi dangin giwa (mammals) da tsuntsaye da dabbobi dangin macizai da kada da kuma kwadi da kifaye ta yi muni fiye da yadda aka yi tsammani a baya.

Kungiyar ta zargi aikace-aikacen bil'adama ga raguwar adadin namun daji ta hanyar lalata muhallansu da wawashe albarkatun kasa cikin sauri ta yadda ba za a iya mayar da su ba.

Rahoton wanda aka gabatar da hadin gwiwar kungiyar kula da dabbobi ta London ya ce namun daji irinsu giwaye a Afirka da kififiya ne suka fi matukar raguwa.