Ban Ki-moon ya nemi a daina tsangwamar likitocin Ebola

Ban ki -Moon Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ban ki -Moon, Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya

Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Mr Ban Ki-moon, ya bukaci kasashe da su guji tsangwamar likitoci da nas-nas da suka taimaka wa marassa lafiyar da ke fama da cutar Ebola, ta hanyar tilasta killace su bayan sun dawo gida.

Da yake jawabi a Addis Ababa, Mr Ban ya ce, irin wadan nan ma'aikatan lafiya mutane ne, na daban da bai kamata a dauki wani mataki da ba na kimiyya ba a kansu, na nesanta su da jama'a.

Kalaman nasa karin kira ne a kan wanda babban jami'in majalisar dinkin duniya kan yaki da Ebola a yankin Afrika ta Yamma, Anthony Banbury, ya yi, inda ya roki gwamnatoci da su guji aikata duk wani abu da zai karya guiwar daruruwan ma'aikatan lafiya da ake bukata su shiga yaki da annobar ta Ebola.