Wata ma'aikaciyar lafiyar ta kamu da Ebola a Amurka

Ma'aikatan jinyar Ebola a Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatan jinyar Ebola a Amurka

Hukumomi a Amurka sunce suna son gudanar da gwajin lafiya a kan dukanin fasinjojin da suka hau jirgi daya da ma'aikaciyar lafiyar nan a Texas wadda ta nuna tana dauke da cutar Ebola.

Ita ce Nas ta biyu da ta kamu da cutar bayan jinyar dan Liberiar da ya mutu sanadiyar cutar ta Ebola.

Ta hau jirgin sama daga Cleveland , Ohio, zuwa Dallas kwana daya kafin ta bayar da rahoton jin alamun cutar.

Shugaba Obama dai ya soke wani balaguron siyasa don mayar da hankali a kan martanin gwamnati a kan barkewar cutar ta Ebola. Badriyya Tijjani Kalarawi ta hada mana wannan rahoton.

Mai magana da yawun kungiyar lafiya ta duniya WHO Dr Chris Dye, ya shaidawa BBC cewa duniya ta shiga wani hali na daban.

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde, yayi kira ga likitoci da ma'aikatan kiwon lafiyar da suka yi murabus da su fito don taimakawa wajen yakar cutar Ebola.