Birtaniya za ta fara gwada fasinjoji

Gwajin fasinja a filin jirgi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwajin fasinja a filin jirgi

Gwamnatin Birtaniya ta ce a ranar Talata za a fara tantance fasinjojin da ke shigowa kasar kan cutar Ebola a filin saukar jiragen sama na Heathrow.

Sakataren harkokin lafiya (Jeremy Hunt) ya ce za yi hakan ne saboda kusan kashi 85 bisa dari na fasinjojin dake shigowa ta nan din daga yankin Afirka ta yamma ne da annobar cutar Ebolar tafi muni.

Darakta Janar na kungiyar lafiya ta WHO Margaret Chan ta ce annobar da ta hallaka mutane fiye da dubu hudu a yankin Afirka ta yamma babban abin damuwa ne.

A halin da ake ciki kuma kafofin watsa labaran Amurka sun bayyana sunan nas din nan Yar Amurka da ta kamu da cutar ta Ebola daga majinyacin nan dan Liberia da ya mutu a asubitin Dallas a matsayin Nina Pham mai yar shekaru 26.