Ministocin tabkin Chadi za su nemi izinin yakar ta'addanci

Shugaba Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan na Najeriya

Ministocin harkokin waje da na tsaro na kasashen da ke da iyaka da tafkin Chadi da kuma Benin sun ce za su mika wa kungiyar Tarayyar Africa da kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin duniya wani kudiri da suka amince da shi.

Kudurin zai share musu fagen tunkarar kungiyoyin da ke tayar da kayar baya a yankunansu.

Kasashen sun amince da wannan kudiri ne a lokacin wani taro na kwana guda da suka kammala dazu a Abuja babban birnin Najeriya.

Ambasada Aminu Wali ministan harkokin wajen Najeriya, ya ce za su mika kudurin ne ga kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya don neman izinin ci gaba da yaki da ta'addanci a kan kungiyoyi irinsu Boko Haram.