Kotu ta daure 'yan Boko Haram shekaru 75

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana zargin kungiyar Boko Haram da kai hare-haren ta'addanci da dama a Nijeriya

Wata babbar kotun tarayya a Legas ta yanke wa wasu 'yan kungiyar Boko Haram uku hukuncin daurin shekaru 75 da aiki mai tsanani.

Mutanen uku da kotu ta samu da laifi, kowannensu zai shafe tsawon shekaru 25 a gidan yari saboda shiga kungiyar ta'addanci.

An gudanar da wannan shari'ah ce cikin sirri saboda bukatar kare rayukan shaidu.

A cewar rahotanni, kotu ta gabatar da hukunci ne a gaban lauyoyi masu gabatar da kara da masu kare wadanda ake kara kadai.