Gwamnati ta hana zuwa aiki a Liberia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rashin isassun kayan kula da lafiyar al'umma na daga cikin matsalolin da ake fuskanta wajen magance Ebola a kasar

Shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf ta sake nanata wani umarni ga ma'aikatan gwamnati da aikinsu bai zama tilas ba, su zauna a gidajensu, a yunkurin shawo kan cutar Ebola.

An kuma umarci Ma'aikatan su shiga aikin wayar da kan jama'a game da cutar Ebola a yankunansu.

A wani al'amarin kuma, daraktan Cibiyar riga-kafin cutuka a Amurka Tom Frieden, ya ce ya yi amanna za a magance cutar Ebola a jikin wani Ba'amurke da ya kamu a Liberia.

Liberiya ita ce kasar da ta fi fama da cutar Ebola, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu uku a yankin Afirka ta yamma.