'Ebola na kama mutane 5 cikin sa'a 1'

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Save the children ta ce ana fuskantar wata annoba da ke yaduwa tamkar wutar daji a Saliyo

Kungiyar Save the Children ta ce an samu kiyasin mutane 765 da suka kamu da cutar Ebola cikin makon jiya a kasar Saliyo, kwatankwacin mutane biyar a duk sa'a guda.

Kungiyar ta ce bukatar kayayyakin kula da lafiya da ma'aikatan jinyar da za su dakile yaduwar Ebola cikin hanzari a Saliyo ta ninka abun da ke akwai.

Bayanai sun ce gadajen kwantar da marasa lafiya 327 ne kadai a fadin kasar, yayin da kananan yara ke mutuwa a cikin gidaje da kan tituna.

Kungiyar ta ce Ebola na yaduwa cikin wani adadi mai razanarwa a fadin kasar Saliyo, inda ake samun ninkawar adadin masu cutar cikin 'yan makwanni.

Ana fargabar cewa, idan lamarin ya ci gaba a haka zuwa nan da karshen watan Oktoba, mutane goma ne za su dinga kamuwa da Ebola a duk sa'a guda.