Cutar Ebola ta bulla a karon farko a Amurka

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Likitoci a Amurka sunce ba zasu bari cutar ta yadu ba

A karon farko an tabatar da bullar kwayar cutar Ebola mai kisa a birnin Texas na Amurka

Jami'ai a wani asbitin birnin sun ce an killace mutumin dake dauke da kwayar cutar.

Ana tunanin cewa mutumin ya kamu da cutar ne a Liberia kafin ya tashi zuwa Amurka kusan makonni biyun da suka gabata.

Mutane fiye da 3,000 ne tuni suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebolan a yammacin Afirka, sannan wasu ma'aikatan agajin Amurka sun warke bayan an kaisu gida Amurkar inda aka yi musu magani.

An sami barkewar cutar Ebolan mafi muni a Liberia wacce ta somo daga makwabciyarta Guinea.

Cibiyoyin Amurka dake yaki da cututtuka sun ce ga alamu an shawo kan kwayar cutar Ebola a Nigeria da kuma Senegal, kasancewar wata guda ke nan yanzu haka ba a sake jin wani da ya kamu da cutar ba.

Hakkin mallakar hoto AP

Sa-ido

Daraktan cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Amurka Thomas Frieden ya fadawa manema labaru ranar Talata cewa 'an gano cewa wani mutum da ya taho daga Liberia na dauke da kwayar cutar Ebola a Amurka'

Kamar yadda Mr Frieden ya ce mara lafiyar wanda ba a bayyana sunansa ba, ya bar Liberia a ranar 19 ga watan Satumba, sannan ya isa Amurka washegari domin ziyartar 'yan uwa, ba tare da nuna alamun kwayar cutar ba.

Alamun cutar sun fito karara ne a rana 24 ga watan Satumba , sannan a ranar 28 ga Satumbar aka kwantar da shi a asibitin Texas, inda aka killace shi.

Ma'aikatan agaji wadanda suka kamu da cutar Ebola a yammacin Afirka sun koma Amurka saboda ayi musu magani, amma wannan shi ne karo na farko da wani mara lafiya ya kamu da cutar a kasar Amurka in ji wakilin BBC Alastair Leithead dake Los Angeles.

Hakkin mallakar hoto AP

Wani jami'in asibitin ya fadawa manema labaru a ranar Talata cewa tuni suka tanadi hanyoyin da zasu magance duk wanda aka kawo shi da irin wannan larura.

Bayanan farko sun nuna cewa mara lafiyar wanda ba a bayyana sunansa ba, wanda kuma lafiyarsa ta tabarbare, baya cikin wadanda suke bai wa masu fama da cutar magani yayinda yake Liberia.

Jami'an lafiya na kokarin lalubo duk mutanen da suka yi mu'amala da mara lafiyar a lokacin da yake dauke da kwayar cutar.

Za a sa musu ido har tsawon kwanaki 21 domin ganin ko wani daga cikinsu zai kamu da zazzabi.

'Zamu dakatar da ita'

A ganin Mr Frieden, abune mai yiwuwa wani mutum kwaya daya a cikin iyali wanda ya yi mu'amala da mara lafiyar ya kamu da Ebolan nan da wasu makonni.

'Amma bani da shakkar cewa zamu shawo kan shigo da cutar, ta yarda ba zata yadu a wannan kasa ba'. Ya kara da cewa 'zamu dakatar da cutar anan'.

Hukumar lafiya da duniya (WHO) ta ce mutane fiye da 3,000 ne suka mutu ya zuwa yanzu, mafi yawancinsu a Liberia.

Tunda farko a ranar Talata, shugaban wata sabuwar hukuma da majalisar dinkin duniya ta kafa domin yaki da cutar ya bukaci a kara daukar matakai cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Anthony Banbury ya fadawa manema labarai a Ghana cewa kashi 70% na mutanen da suka kamu da cutar na bukatar a basu magani, kuma dole ne a binne kashi 70% na wadanda suka mutu cikin watanni biyu karkashin tsaftataccen yanayi.

Wannan ita ce barkewar kwayar cuta mafi muni a duniya.