Kerry: A kai zuciya nesa a Hong Kong

Hakkin mallakar hoto EPA

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi kira ga mahukunta a Hong Kong da su kai zuciya nesa kan masu zanga-zangar kare mulkin dimokradiyya a yankin, bayan kwanakin aka shafe ana gudanar da zanga-zangar.

Yayinda yake maida martani kan kalaman na Mr Kerry,ministan harkokin wajen China Wang Yi ya ce kasashen duniya kada su yi katsalandan kan harkokin cikin gida na kasar.

Shugabannin dalibai a Hong Kong sun yi barazanar mamaye gine-ginen gwamnati muddin shugaban na Hong Kong CY Leung bai sauka daga mukaminsa ba ranar Alhamis

Tsohon gwamnan Hong Kong, Chris Patten ya musanta cewa wasu ne daga waje ke kitas zanga-zangar.