Microsoft ya sanarda Manhajar Windows 10

Hakkin mallakar hoto microsoft
Image caption Microsoft ya kirkiri Windows 10 ne a wannan lokaci saboda Windows 8 bai samu karbuwa ba sosai

Kamfanin Microsoft ya sanarda bayanan farko na abubuwan da sabuwar babbar manhajar Windows 10 da kamfanin ke shirin kaddamar wa za ta kunsa.

Sunan sabuwar manhajar ya ba mutane mamaki, saboda yadda aka tsallake daga manhajar Windows 8 zuwa Windows 10.

Sabuwar manhajar Windows 10 za tayi aiki a na'urorin daban-daban, da suka hada da manyan wayoyi, da kwamfutoci, da kuma wasannnin kwamfuta na Xbox, da za su rika sayen manhajoji daga kasuwa guda.

Sabuwar manhajar Windows 10 ta dawo da hanyar fara shiga, da sarrafa kwamfuta wato (Start Menu), wadda babu a manhajar Windows 8.

Kazalika, an tsara manhajar Windows 10 ta yadda za ta iya daukar manhajojin kaddamar da ayyuka daban-daban da mutane suka fi amfani da su.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Windows 10 ya yin kama da windows 8 wajen numa manhajoji a fuskar kwamfuta

An kuma tsara manhajar Windows10 ta yadda masu amfani da ita za su iya ganin alamun sakonnin Email, dana Facebook da kuma hasashen yanayi cikin sauri.

Manhajar ta Windows 10 ta na yin kama da ta Windows 8 wajen nuna manhajojin kaddamar da ayyuka a fuskar kwamfuta, kuma kamfanin Microsoft ya ce anyi hakan ne saboda kada ta zamo wani sabon abu ga masu amfani da Windows 8 da Windows 7.

Mutane da dama dai sun soki manhajar Windows 8 saboda ta banbanta da wadda akafi sabawa da ita wato Windows 7, abinda ya sa ma'aikatu da yawa suka ki yin amfani da ita.