An maka uwargidan shugaban Zimbabwe a kotu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban kasar na zargin rashin bin ka'ida wajen bai wa Grace Mugabe shaidar kammala karatu

Kungiyar dalibai a Zimbabwe mai suna Zinasu ta gurfana a gaban kotu a Larabar nan a kokarinta na samun karin bayani a kan bai wa mai dakin shugaban kasar, Grace Mugabe shaidar digirin digirgir.

Wani dalibi mai fafutuka, Samuel Gwenzi ya ce kare kimar ilmi a Zimbabwe, abu ne mai muhimmanci.

Wasu mutane na cewa da mamaki yadda Mai dakin shugaba Mugabe ta kammala cikin sauri, yayin da wasu ke cewa ba ta shaidar digirin, wani bangare ne na yunkurinta na zama shugaban kasar.

Wata jarida gwamnatin kasar, the Herald ta ce mai dakin shugaban kasar ta karbi shaidar digirin ne a fannin nazarin sauya tsarin zamantakewa da ayyukan iyali.