Tabbas mun kashe Shekau –Sojin Nigeria

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau

Shalkwatar tsaron Nigeria ta sake jaddada cewa ta kashe Abubakar Shekau da ma wani da ke shigar burtu yana cewa shi ne Shekau.

Ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, domin mayar da martani ga wani bidiyo da kungiyar Boko Haram ta fitar da ke nuna cewa Abubakar Shekau yana nan da ransa, sabanin ikirarin sojojin Nigeria.

Shalkwatar tsaron Nigeria ta ce a nazarin da ta yi ga alama siddabaru ne kawai bidiyon da Boko Haram ta fitar da ke nuna cewa Shekau yana raye.

Rundunar sojin Nigeria ta ce a nazarin da ta yi, hoton bidiyon bai nuna lokacin da aka dauke shi ba, ko kuma wata alama da ke nuna wa karara Shekau na raye.

Ta ce hoton bidiyon bai yi bayani kan wani sabon abu da ya faru ba, tun bayan lokacin da sojoji suka ce sun kashe wanda yake shigar burtu da sunan Shekau.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau

Sanarwar shalkwatar tsaron Nigeriar ta kuma ce, abun lura a nan shi ne jirgin saman da aka ambata a bidiyon ya bata ne tun kafin a kashe mai kwaikwayon Shekau, don haka babu mamaki idan 'yan ta'addan suka yi siddabaru da hotunan bidiyo ko kuma suka watsa wani hoton bidiyo da aka nada tuntuni, don su nuna cewa Shekau bai mutu ba.

Rundunar sojin Nigeriar ta kuma jaddada cewa, tun a watan Satumbar da ya gabata ne sojoji suka kashe mutumin da ke fitowa a hotunan bidiyo yana ikirarin cewa shi ne Abubakar Shekau.

Sannan mutanen da suka san shi sun tabbatar da cewa shi ne. Sai dai rundunar sojin Najeriyar ta ce, yayinda ta ke ci gaba da tattara bayanai da kuma jiran ganin sabon bidiyon, sakonta ga 'yan Boko Haram shi ne, za su dau matakin hukunci a kan duk wanda ke amsa sunan Shekau ko aiki irin nasa.