Burtaniya ta nemi karin tallafi kan Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana dai ta bayyana damuwa game da karancin kayan kula da lafiya don yaki da cutar a Liberiya da Saliyo

Burtaniya ta yi kira ga kasashen duniya su tallafa wa yaki da cutar Ebola da ta addabi wasu kasashen Afirka ta yamma.

Da yake jawabi a wani taron hadin gwiwar Burtaniya da Saliyo a kan Ebola, ministan harkokin wajen Burtaniya, Philip Hammond ya ce akwai bukatar karin kudade, likitoci da ma'aikatan jinya don shawo kan yaduwar cutar.

Rahotannin baya-bayan nan a Saliyo na cewa cutar Ebola tana yaduwa cikin hanzari tamkar wutar daji, kuma fiye da duk yadda ake tsammani.

Haka zalika, Jami'in majalisar Dinkin Duniya kan yaki da Ebola, Anthony Banbury ya ce cutar ta kai ga kusan kowanne yanki a kasar Liberiya.