Musulmi miliyan biyu sun fara aikin hajji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hawan dutsen arfa da za a gudanar a gobe juma'a, muhimmin bangare ne na aikin hajji

A Alhamis din nan ne, musulmi miliyan biyu da suka je Saudiyya daga kasashe daban-daban suka fara gudanar da aikin hajjin bana a garin Makkah.

A ranar farko ta aikin hajjin, musulmi cikin farin mayafai na tafiya zuwa Minna daga garin Makka, mahaifar Annabi Muhammadu (S.A.W), inda za su shafe daren Alhamis din nan a cikin manyan tantunan da aka tanada.

Sannan kuma a ranar Juma'a su yi tsayuwar dutsen arfa, wani muhimmin bangare na ibadar aikin hajji.

Tun da farko, Hukumomin Saudiyya sun nuna damuwa a kan cutukan Ebola da Mers, don haka suka karfafa daukar matakan lafiya.

Haka zalika, Hukumomin Saudiyya sun hana takardun zuwa Hajji da na aiki ga mutanen kasashen uku na yankin Afirka ta yamma da suka fi fama da cutar Ebola a wani bangare na riga-kafi.

Kasashen su ne Saliyo da Guinea da kuma Liberiya.