Julia Pierson tayi murabus

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Julia Pierson ta dauki alhakin sakaci na kyale Gonzalez ya shiga White House da wuka

Daraktar hukumar tsaron farin kaya ta Amurka, Julia Pierson ta yi murabus, kwana guda bayan ta dauki alhakin barakar tsaro da aka samu a fadar shugaban kasar.

A makon daya gabata ne wani mutum dauke da wuka, ya kutsa cikin fadar ta White House, ta wata kofa da ba a kulle ba, inda sai da ya kusa shiga sasan da shugaba Obama ya ke kafin aka samu cafke shi.

Julia Pierson tayi murabus ne bayan da aka gano ba gaskiya ba ne bayanan da hukumar ta, ta bayar daga farko, cewa an hana mutumin mai suna Omar Gonzalez shiga fadar ta White House.

Omar Gonzalez ya ratsa ta dakuna da dama har ya samu wucewa ta wata matakala ta shiga sasan shugaba Obama, kafin jami'an tsaro su kamashi.

An zabi Joseph Clancy, wani tsohon ma'aikacin hukumar tsaron ta farin kaya a matsayin darakta na wucin gadi.