Sabuwar hanyar cajin batirin salula

Image caption Za a rika cajin wayoyin salula kyauta ne a rumfunan,

Za a mayar da rumfunan da ake wayar tarho a kan hanyoyi zuwa wuraren cajin wayoyin salula masu amfani da hasken rana a London.

A wannan makon ne aka fara amfani da shida daga cikin irin wadanda rumfuna a babban titin Tottenham Court Road a London.

Kyauta ne za a rika cajin batiran wayoyin salula a rumfunan, sai dai mutane za su rika ganin tallace-tallace yayin da su ke jiran wayar su ta yi caji.

Da dama daga cikin irin wadannan rumfunan a Burtaniya ba sa aiki, koda ya ke an mayar da wasu daga cikin su dakunan karatu, wasu kuma aka sanya kayayyakin kiwon lafiya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An kuma tanadi wurare da dama don cajin wayoyin salula iri-iri

An kuma tanadi wurare da dama don cajin wayoyin salula iri-iri da kuma talbijin da ke nuna tallace tallace a cikin rumfunan.

Wasu dalibai biyu da suka karanci fannin yanayin kasa, Harold Craston da Kirsty Kenny ne su ka kirkiro da wannan tsari.

A halin yanzu wadannan daliban na karatu ne a makarantar nazarin tattalin arziki da ke birnin London, kuma suna da sha'awar nemo hanyoyin da za a bi don takaita wuraren da jama a ke amfani da su.

Akalla mutane shida ne ke amfani da wuraren kowace sa'a guda tun bayan da aka kaddamar da shi.