Ina nan a raye –Shekau

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi watsi da ikirarin rundunar sojin Nigeria na cewa ya mutu, a wani sabon faifan bidiyo da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu ranar Alhamis.

Shekau ya fada a cikin hoton bidiyon na minti 36 cewa "Ina nan a raye. Zan mutu ne kawai ranar da Allah ya dauki raina."

Ya kara da cewa kungiyarsa na gudanar da iko kan daular musulunci da aiwatar da hukunce-hukuncen shari'ah a garuruwan da ta kwace.

A makon jiya ne, rundunar ta ce an harbe mutumin da yake shigar burtu da sunan jagoran Boko Haram Abubakar Shekau yayin fafatawa a garin Kunduga na jihar Borno.

Ko da yake, masu sharhi kan al'amuran tsaro da Amurka sun bayyana shakku a kan sahihancin ikirarin rundunar sojan Nigeria.

Sabon hoton bidiyon ya nuna Shekau sanye da kayan yaki da bakin takalmi sau-ciki, tsaye a bayan wata mota a-kori-kura yana harba bindigar kakkabo jiragen sama a iska.

Daga nan sai ya tsaya a gaban wasu motoci guda uku a tsakiyar wasu mayaka hudu da suka rufe fuskoki, dauke da muggan makamai, ya yi jawabi cikin harshen larabci da Hausa tsawon mintuna 16.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau

Abubakar Shekau da yalwar gemu, kamar yadda ya saba bayyana a hotunan bidiyo na baya, ya ce ikirarin sojin Nigeria cewa ya mutu farfaganda ce kawai.

"Babu abun da zai kashe ni, sai kwanana ya kare... Har yanzu ina raye. Wasu suna tambaya wai shekau rai biyu ne da shi. A'a, da ikon Allah rai daya ne da ni" ya fada ga alama yana karantowa a takarda.

A baya, sau biyu dakarun tsaron Nigeria suna cewa Shekau ya mutu, daya a shekara ta 2009 lokacin wani yamutsi a Maiduguri sai kuma a bara.

Kungiyar ta kuma yi ikirarin harbo jirgin yakin Nigeria, da ya bata kimanin makwanni uku da suka wuce.

Sai dai, wani mai magana da yawun rundunar sojin saman Nigeria, Air Commodore Dele Alonge ya ce farfagande ce kawai da zance maras tushe, wata kungiya ta ce ta kakkabo jirgin na yaki.

Hoton bidiyon ya kuma nuna yadda aka jefe wani mutum a kan laifin zina, wani kuma aka yanke masa hannun dama a kan sata.

An kuma ga yadda aka yi wa wani mutum da wata mace bulala 100 kowannesu, su ma dai a kan yin zina.

An ga cincirindon mutane ciki har da mata da kananan yara na kallon yadda ake zartar da wadannan hukunce-hukunce.

Game da jirgin saman yakin kuma, an ga mayakan Boko Haram suna leke-leke a cikin tarkacen jirgin kirar Alpha da aka kakkabo, kuma ana iya ganin tambarin kore da fari na sojan Nigeria karara a jikinsa.