Amurka ta soki Israila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka ta ce Israila na iya rasa goyon bayan da ta ke samu daga kasashen duniya.

Amurka ta ce akwai alamar tambaya kan manufofin Israila akan Palasdinawa.

Gwamnatin Amurka ta bayyana haka bayan ganawar da Firaministan Isra'ila Benjamin Mr Netanyahu ya yi da Shugaba Barack Obama tun bayan rikici na baya bayan nan a Gaza.

Shugaba Obama ya ce tilas a samu sauyi kan banbance-banbancen da ke tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

'Yan sa'o'i bayan ganawar ce kakakin fadar White House Josh Earnest, ya yi kakkausar suka kan shirin Israila na ci gaba da gine gine a yankunan data mamaye.

Amurkar ta gargadi Israilan da cewa tana iya rasa goyon bayan da ta ke samu daga kasashen duniya.

Tun da farko yayin da ya ke magana a wani taron manema labarai na hadin guiwa da shugaba Obama, Mr Netanyahu ya ce a shirye ya ke wajen kokarin neman zaman sulhu da Palasdinawa.