An kara dokar hana zirga-zirga a Borno da Yobe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin sun dauki matakin ne domin kare hare-haren Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya ta bakwai mai mazauni a birnin Maiduguri na jihar Borno ta kara wa'adin dokar hana zirga-zirgar ababan hawa a yankunan ikonta har zuwa ranar Talata.

A da dai dokar da sojin suka sa wadda ta shafi masu ababan hawa a jihohin Yobe da Borno ta fara ne daga ranar Juma'a zuwa yau Litinin, amma kuma sai rundunar sojin ta fitar da wata sanarwa ranar Lahadi cewa ta kara tsawon dokar har zuwa Talata da karfe bakwai na safiya.

Sakamakon dokar jama'a a birnin Maiduguri suna bikin babbar Sallah ba tare da walwala ba sosai kuma lamarin ya shafi harkokin kasuwanci kamar yadda wasu mazauna birnin suka ce.

Haka kuma dokar ta shafi harkoki a babban birnin jihar Yobe ma, Damaturu har ma da sauran garuruwan jihar.

Rundunar ta ce matakin ya biyo bayan bankado wani shiri na kaddamar da jerin hare-hare a birnin Maiduguri ne na jihar Borno lokacin shagulgulan babbar sallah.

Ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewa kungiyar Boko Haram ta shirya kai hare-hare a wuraren da suka hadar da masallatan Idi da kasuwanni da wuraren zaman jama'a.

Karin bayani