David Cameron ya kai ziyara Afghanistan

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Za a gudanar da wani taro kan bai wa Afghanistan gudunmawa cikin watan gobe a London

Firaministan Burtaniya, David Cameron ya zama shugaban kasa na farko a duniya da ya gana da sabon shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani da aka rantsar kan mulki ranar litinin.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan tattaunawa a Kabul, Cameron ya ce Burtaniya ta ba da gagarumar gudunmawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a Afghanistan.

Ya kuma ce za ta ci gaba da tallafa wa bangarorin ilmi da ayyukan lafiyan kasar, bayan kammala aikin rundunar tsaro ta Nato na yanzu nan gaba a wannan shekara.

An amince da kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Afghanistan bayan doguwar tattaunawa sakamakon dambarwar da aka tafka kan zaben shugaban kasar.