'Yan sanda sun raba aure a Indiya

Image caption Rahotanni sun ce an daura auren ne ba tare da amincewar iyayen amarya ba

'Yan sanda a tsakiyar Indiya sun ayyana wani aure tsakanin wani kirista da wata mai bin addinin Hindu a matsayin haramtacce.

Bayanai sun ce Hukumomin 'yan sanda sun fuskanci matsin lamba kan wannan lamari daga kungiyoyin Hindu masu tsaurin ra'ayi.

Matasan ma'auratan daga Madhya Pradesh sun gudu, inda suka aurar da kansu a wani shagalin auren Hindu ba tare da amincewar iyayen amaryar ba.

Da kungiyoyin Hindu suka bayyana adawa tare da yin barazanar kai hari kan gine-ginen gwamnati, sai 'yan sanda suka bi sawun ma'auratan kuma suka tilasta musu rabuwa.

Rahotanni sun ce irin wadannan matakai daga kungiyoyin Hindu na kara zama ruwan dare a watannin baya-bayan nan.