Shugaban Goodluck Jonathan
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar bangaranci a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty

Ranar daya ga wananan watan Oktoban ne Najeriya ta cika shekaru 54 a matsayin kasa mai 'yancin kanta.

Kuma a yau shekaru dari kenan da turawan mulkin mallaka suka hade kudanci da arewacin kasar.

Sai dai har yanzu hadin kai tsakanin al'umar kasar ya gagara.

Shi kansa shugaban kasar Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana cewa har yanzu makomar Najeriya ta fuskar curewa wuri guda na tangal-tangal.

Kuma wannan, a cewarsa shi ne babban abin da ke ci gaba da daure-kai, tare da jefa kasar cikin duhu.

Wasu 'yan arewacin kasar dake kudancin kasar na cewa ana nuna masu bambanci; hakazalika suma 'yan kudancin kasar dake arewa suna cewa ana maida su 'ya'yan bora.

Menene asalin wannan matsalar kuma ta yaya za a magance ta?