Musulmi na bukukuwan babbar sallah

A yau musulmin duniya suka fara shagulgulan bikin babbar salla ta layya.

Layya aiki ne na ibada wanda ya samo asali daga Annabi Ibrahim Alaihissalam,wanda kuma malamai ke cewa na koyar da darussa na rayuwa da dama.

Daga cikin fa'dodin layya da malamai kan fadakar akai akwai nuna biyayya ga Allah.

A ranar alhamis din da ta gabata ne alhazai suka isa Minna, kuma da safiyar juma'a suka dunguma zuwa dutsen Arafat.

Dubun dubatar mahajjata ne suka fita zuwa dutsen na Arafat, domin wannan zama da ke matsayin jigo na aikin hajji.

Sakamakon hawan Arafata din ranar Juma'a su kuma sauran al'ummar musulmi na duniya suke sallar layya a yau Asabar.