Kotu ta nemi rufe asibitocin zubar da ciki

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Damar zubar da ciki, 'yanci ne da tsarin mulkin Amurka ya bai wa 'yan kasar

Wata kotun daukaka kara ta tarayya a Amurka ta ba da hukuncin cewa ana iya tsaurara haramci a kan asibitocin zubar da ciki a jihar Texas.

Ana tsammanin matakin a kan gagarumin ikon dokar zubar da ciki ta 2013, zai rufe dukkanin asibitocin zubar da ciki ban da guda bakwai a jiha mafi yawan jama'a a Amurka.

'Yan jam'iyyar Republican da sauran masu ra'ayin 'yan mazan jiya a Texas sun ce dokar za ta kare lafiyar mata.

Sai dai masu sukar lamirin batun na cewa dokar wani matakin haramta zubar da ciki ne ta hanyar bayan gida.

Suka ce zubar da ciki, 'yanci ne da tsarin mulkin Amurka ya bai wa 'yan kasar tun bayan muhimmin hukuncin babbar kotun kasar a 1973.