'AIDS ta bullo ne daga Kinshasa'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gagarumar harkar sufurin jirgin kasa a Kinshasa ta taimaka wajen yaduwar cutar AIDS ko SIDA

Masana kimiyya sun ce cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS) ta faro ne daga birnin Kinshasa a shekarun 1920.

Masanan na kasashen duniya sun ce hauhawar yawan jama'a da aka samu da yawan jima'i da harkar sufurin jirgin kasa a lokacin a kasar ta DRC a yanzu su suka haddasa yaduwar cutar.

Kwararrun masanan sun fitar da sakamakon wannan binciken ne a mujallar kimiyya ta Science.

Masanan sun yi amfani da samfurin da aka adana na alamun yadda cutar ta samo asali ne.

Ayarin masanan daga jami'ar Oxford da kuma ta Leuven da ke Belgium sun kuma yi kokarin gano inda ainahin asalin kwayar cutar ya faro kafin Kinshasan.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu ana kan neman maganin kwayar cuta mai karya garkuwar jiki

Rahoton ya ce gagarumin karuwar jama'a da jima'i da amfani da alluran asibiti da ba a tsaftace su a lokacin da alamu su suka habaka cutar.

Bayan haka kuma a lokacin akwai mutane kusan miliyan daya da ke zirga-zirga ta hanyar jiragen kasa da kasar Belgium ta samar a lokacin wadanda ke bi ta Kinshasan zuwa wasu kasashe a yankin.

Kwayar cutar HIV ta dauki hankalin duniya a wuraren 1980 kuma ta kama mutane kusan miliyan 75.

Ita dai kwayar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV wani nau'i ne na cutar gwaggon biri, wadda ake ganin ta sauya ta shafi mutane ta hanyar taba jinin da ke dauke da kwayar wajen farautar namun daji.