Mayakan IS sun kashe dan Birtania

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Alan Henning shi ne dan Birtania na biyu da mayakan IS suka datse wa kai

Mutane da dama na ci gaba da Allah-wadai da kashe dan Birtaniya Alan Henning da kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulnci ta yi.

A watan Disambar bara kungiyar ta kama Mr. Henning mai shekaru 47, wanda kuma asalinsa matukin tasi ne yayin da yake taimakawa wajen kai kayan agaji zuwa Syria.

Rahotanni na cewa mutumin da ya bayyana a hoton bidiyon kisan Mr Henning, rufe da fuskarsa, yana magana ne da harsehn turanci daidai da wanda ya bayyana a sauran hotunan bidiyo da suka gabata.

A baya bayan nan kungiyar ta IS ta kashe wasu 'yan jaridar Amurka guda biyu da suka hada da James Foley da Steven Sotloff da kuma wani dan yankin Scotland da ake kira David Haines.

Firaministan Birtania David Cameron ya jagoranci shugabannin duniya wajen Allah-wadai da ksan, yana cewa rashin imanin 'yan IS ba shi da iyaka, kuma za a yi kokarin gano masu kisan a hukunta su.

Wakilin BBC ya ce "har yanzu kungiyar na rike da wani mai daukan hoto, dan asalin kasar Birtaniya dake ake kira John Kentling."