Ana ci gaba da bukukuwan babbar sallah

Al'ummar musulmin duniya na ci gaba da bikin babbar salla ko sallar layya bayan da aka yi hawan arfa ranar Juma'a da ta gabata.

A lokacin bikin na wananan salla ta layya musulmin da suka samu damar yanka dabbobi sukan yi sadaka da naman da kuma raba abinci ga 'yan uwa da abokan arziki da sauran jama'a.

Layya aiki ne na ibada wanda ya samo asali daga Annabi Ibrahim Alaihissalam,wanda kuma malamai ke cewa na koyar da darussa na rayuwa da dama.

Daga cikin fa'idodin layya da malamai kan fadakar akai akwai nuna biyayya ga Allah.

Sakamakon hawan Arafat din ranar Juma'a da miliyoyin mahajjata suka yi kuma sauran al'ummar musulmi na duniya suke sallar layya a ranar Asabar.