Somalia: Sojoji sun kwace garin Baraawe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al -Shabab ta samu babban komabaya bayan kwace garin Baraawee

Sojojin Somaliya, tare da hadin-gwiwa da rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka sun yi nasarar kwace iko da garin Barawe daga hannun Kungiyar Alshabab, wanda kuma shi ne gari na karshe a tsakanin muhimman sansanonin kungiyar.

Garin Barawe, wanda ke bakin ruwa na da tazarar kilomita kusan 200 daga Mogadishu, babban birnin kasar

Garin ya shafe shekara 6 a hannun kungiyar Alshabab.

Kwace garin wani babban komabaya ne ga kungiyar mai son kwace iko a Somalia.

Mayakan kungiyar Al-Shabab na amfani da garin wajen kai hari kan Mogadishu da kuma hanyar shigo da makamai.

Mazauna garin sun ce mayakan Al-Shabab sun tsere daga garin bayan farmakin sojojin.