Kamaru:Taron C' wealth karo na 60

Cameroon Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shine karon farko da Kamaru za ta karbi bakuncin taron

Kasar Kamaru na karbar bakuncin babban taron 'yan majalisun dokokin kasashen kungiyar Commonwealth.

Taron wanda yake gudana a karo na 60 za a fara shi ne a yau litinin inda kimanin wakilai 800 daga kasashe 53 za su halarta.

Za a kwashe kwanaki biyar ne a wannan taro inda za a duba batutuwa da suka shafi matsayin majalisar a tsakanin kasashe da tafiyar da mulki.

Haka kuma taron zai yi dubi a kan hakkin mata da tunawa da matasa da ci gaban su.

Wannan shine karo na farko da Kamaru ke karbar bakuncin wannan taro tun bayan da ta shiga kungiyar a shekarar 1995.