An gano sabbin tsaunuka a teku

Mountocean Hakkin mallakar hoto D.SANDWELL.SCRIPPS
Image caption Masu bincike sun ce dan adam bashi da cikakken ilimin kan abin da yake karkashin ruwa

Wasu masu binciken hadin gwiwa na Amurka da na nahiyar turai, sun ce sun gano wasu sabbin tsaunuka a karkashin teku.

A cewar masu binciken tsayin tsaunukan zai kai akalla tsawon kilomita 1.5.

Sun kara da cewa dalilin da ya sa ba a san da zamansu ba saboda suna karkashin ruwa ne.

Masu binciken da suka hada da Farfesa Dave Sandwell da wasu abokanan aikinsa, sun yi amfani ne da fasahar tauraron dan adam suka gano tsaunukan.

An wallafa sakamakon binciken ne a wata mujallar kimiyya mai suna Science Magazine.

A cewar Sandwell, a binciken farko da suka gudanar, sun gano akalla tsaunuka 5000.

"Mai yuwuwa hakan bai zai zamanto wani babban ci gaba ba, amma yawan tsaunukan dake karkashin teku wadanda ake gano su na karuwa." In ji Sandwell

Ya kuma kara da cewa akwai yuwuwar a samu karin yawan tsaunuka da adadinsu zai kai 25,000 anan gaba.

A cewar masu bincike a duniya akwai karancin ilmin abubuwan dake farfajiyar karkashin teku.