Ebola ta bayyana a Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatan lafiya dauke da Miguel Pajares malamin kirista na Spain da Ebola ta hallaka bayan ya je Saliyo

Ministar lafiya ta Spain ta tabbatar cewa wata ma'aikaciyar jinya a wani asibiti a babban birnin kasar Madrid, wadda ta kula da wani malamin kirista da Ebola ta hallaka, ita ma ta harbu da kwayar cutar.

Ma'aikaciyar jiyyar ita ce ta farko a wajen nahiyar Afrika da ta kamu da wannan cuta da ta zama annoba.

Ministar, Ana Mato, ta ce, maaikaciyar tana daga cikin wadanda suka kula da Manuel Garcia Viejo mai wa'azin kirista, wanda ya mutu a watan Satumba bayan ya je Saliyo.

Ta kuma kula da Miguel Pajare da shi ma malamin kiristan ne, da shi kuma ya mutu a watan Agusta sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

A makon da ya gabata ne Ma'aikaciyar wadda ba a bayyana sunanta ba ta fara rashin lafiya a lokacin da take hutu.

Ministar ta ce yanayin da matar take ciki bai yi tsanani ba, yayin da ake kula da mutane da dama da suka yi mu'amulla da ita da kuma sauran abokan aikinta.