Shirin biyan kudi ta Facebook

Facebook Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dalibi a Amurka ne ya fara gwada shirin biyan kudin ta Facebook

Shafin Facebook zai fara bai wa masu amfani da shafin damar biyan kudade ta cikinsa.

Wani dalibin ilimin kimiyyar kwamfuta a Amurka ne ya fara gwada wannan tsari, wanda dama ce da za ta zo ga masu amfani da shafin na Facebook nan ba da jimawa ba.

A baya Mark Zuckerberg, mutumin da ya kirkiro shafin na Facebook, ya taba cewa akwai yuwuwar a samar da damar ta biyan kudade ta shafin.

Ko da yake Facebook din ya ki cewa uffan game da wannan batu a yanzu.

Dalibin mai suna Andrew Aude, mai shekaru 21 ya aike da hoton biyan kudi ne ta Twitter.

Rahotanni sun ce ya gano manhajar ce ta hanyar da ake ke bai wa masu kirkirar shafuka su sauya manhajoji.

A hoton da ya aike, ya hada har da bayanan da ke jikin katin cire kudi na banki wanda hakan kan iya ba da damar aikawa da kudade.

Sai dai a wata ganawa da Zuckerberg ya yi da masu zuba jari a watan Yulin da ya gabata, ya ce kamfanin na Facebook na da ayyuka da dama a gabansa da zai kammala kafin ya tunkari batun samar da damar biyan kudaden ta hanyarsa.

"Za mu dauki lokaci kafin mu aiwatar da wannan shiri, za kuma mu yi iya bakin kokarinmu mu ga cewa idan mun aiwatar da shirin ya zama mai dorewa."