Shugaba Kenyatta ya ce zai je kotun ICC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce ba ya fargabar komai

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya shaida wa majalisar dokokin kasar a Nairobi cewa zai halarci zaman Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) a Hague.

Kotun ta ICC ta mika masa sammaci ya gurfana a gabanta ranar Laraba don ya yi bayani a kan zargin cewa an rike shaidar da ake da ita game da shi.

Ana dai zargin Mista Kenyatta da shirya kisan kiyashin kabilanci bayan zaben shekara ta 2007.

Ya shaida wa majalisar dokokin cewa ba shi da wata fargaba, kuma ba shi da laifi a kan duk wani zargi game da shi.

'Yan majalisar dokokin Kenyar kusan 100 ne ke shirin tafiya Hague domin goya masa baya.

Karin bayani