Sojojin Somalia sun karbe Barawe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kubucewar Barawe babbar koma-baya ce ga kungiyar Al-Shabaab

Sojojin kasar Somalia tare da goyon bayan dakarun Kungiyar Kasashen Africa, wato AU, sun ce yanzu haka su ne ke da cikakken iko da garin Barawe—gari na karshe da ke gabar teku, inda 'yan kungiyar Al-Shabaab suka yi kakagida.

Da safiyar ranar Litinin an yi ta jin karar harbe-harbe lokacin da sojojin suka kutsa kai zuwa cikin garin.

Rahotanni sun ce a yanzu kura ta lafa, kuma tankokin yaki da motocin sulke na sintiri akan tituna.

Garin na Barawe ya shafe shekaru ashirin da uku ba ya karkashin ikon gwamnatin tarayyar kasar ta Somalia, kuma kungiyar Al-Shabaab ta shafe shekaru shida tana iko da shi.

Gabanin wannan farmaki, mayakan kungiyar ta Al-Shabaab sun fara janyewa daga garin tun a makon jiya.

Gwamnan yankin da sauran jami'an soji sun yi jawabi ga mutanen garin suna kira da a kwantar da hankali, suna ikrarin cewa mulkin kungiyar Al-Shabaab ya zo karshe.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce 'yan kungiyar ta Al-Shabaab kan janye idan suka fuskanci gagarumin hari, amma su kan bar wadansu mayakan a tsakanin fararen hula don su kaddamar da hare-hare daga bisani.