Akwai 'yan wasa nagari ko Eto'o ya tafi

Image caption 'yan wasan Kamaru masu tasowa sun fara nunawa duniya suma za a je da su

Tsohon dan wasan kwallon kafan Kamaru, Patrick Mboma, ya ce a rashin Samuel Eto'o, sabbin 'yan wasan gaba da za a samu za su yi rawar gani.

Tsohon Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Kamaru, Eto'o mai shekaru 33, ya daina bugawa kasar kwallo a watan Agusta bayan shekaru 18.

Mboma ya shaidawa BBC cewa ba abin jin dadi ba ne murabus din na Eto, ganin cewa dan wasa ne haziki.

''Amma tun da ya nuna zai yi murabus, Eric-Maxim Choup-Moting da Vincent Aboubakar sun fara nuna wa duniya su ma 'yan wasa ne da za a je da su,'' Mboma ya ce.

Aboubakar, wanda ke bugawa Porto wasan gaba, ya zura kwallo uku a raga a wasanni biyu na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afrika a 2015.

Choupo-Moting kuwa ya fara bugawa kungiyar Schalke 04 da kafar dama a gasar Bundesliga inda ya zura kwallo uku a wasanni bakwai.