Shugaba Kenyatta zai bayyana a kotu

Shugaba Uhuru Kenyatta Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta zai gurfana a kotun manyan laifuka ta duniya dake Hague a ranar laraba inda zai fuskanci zarge zargen aikata laifuka akan bil adama.

Mr Kenyatta -- wanda zai kasance shugaban kasa na farko da zai je gaban kotu -- na fuskantar tuhumar shirya kisan kabilanci sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar shekaru bakwai da suka wuce.

Shi dai shugaba Kenyatta ya musanta zargin.

Kotun ta ICC ta mika masa sammaci ne domin ya yi bayani game da zargin cewar an rike wasu shaidu kansa.

Antoni Janar na kasar ta Kenya -- wanda ya bayyana a gaban kotun a yau, Talata -- ya musanta zargin daga mai gabatar da kara cewar gwamnatin Kenya ba ta mika shaida ba.