ICC ta shirya wa gurfanar Kenyatta

Image caption Kenyatta ne shugaba na farko mai ci da zai gurfana a gaban ICC

Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya ta shirya tsaf don fara zaman kwanaki biyu na sauraron shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, da zai zamo shugaban kasa mai ci na farko da ya gurfana a gabanta.

Shugaba Kenyatta yana fuskantar tuhuma a kan zargin iza wutar rikicin da ya biyo bayan zaben 2007 inda aka kashe mutane fiye da 1,000.

Lauyoyin da ke kare shugaban sun bukaci ayi watsi da karar.

Alkalan kotun za su saurari bayanan dukkan bangarori biyu da ke cikin shara'ar.

Mista Kenyatta ya mika ragamar shugabancin kasar ga mataimakinsa William Ruto, har sai ya dawo daga zaman kotun na kwanaki biyu.

Kotun ta ICC ta bukaci Shugaba Kenyata ya gurfana ne domin ya yi bayani a kan zargin cewa ya ki ya bari a kai shaidan da za at tabbatar da hannunsa a tuhumar da ake masa.