INEC ta ce za ta martaba umarnin kotu

Image caption Da farko, hukumar zaben Nigeria ta sanya Asabar 11 ga wannan wata a matsayin ranar zaben cike gurbi

Hukumar zabe ta kasa a Nigeria INEC, ta ce za ta yi aiki da hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda ya umarci dakatar da zaben cike gurbi na gwamnan Adamawa.

Tun da farko, hukumar ta tsara gudanar da zaben cike-gurbin a ranar Asabar mai zuwa.

A Larabar nan ce dai, kotun ta yanke hukunci a karar da mataimakin gwamnan jihar Barista Bala James Ngilari, ya shigar inda ya bukaci a ba da umarnin rantsar da shi a matsayin gwamna.

Ya ce bai gabatar da takardar yin murabus ga tsohon gwamna Murtala Nyako kafin majalisar dokokin jihar ta tsige shi ba.

Sai dai, mukaddashin gwamnan jihar Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa ba zai sauka daga mukamin domin a rantsar da Ngilari a gwamna ba.