INEC ta dakatar da zaben cike-gurbi a Adamawa

Image caption Tun da farko, Hukumar zaben ta ce za ta mutunta umarnin kotun tarayyar

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria ta dakatar da duk shirye-shiryen gudanar da zaben cike-gurbi a kujerar gwamnan jihar Adamawa.

Wata babbar kotun tarayya ce ta ba da umarnin dakatar da zaben cike-gurbi bayan ta yanke hukunci rantsar da tsohon mataimakin gwamnan Adamawa a kan mukamin gwamna.

Kotun ta ce rantsar da Ahmed Fintiri a matsayin gwamnan riko a jihar Adamawa ya saba tsarin mulkin kasar.

Tun da farko, hukumar INEC ta sanya Asabar 11 ga wannan wata a matsayin ranar gudanar da zaben cike-gurbin gwamna Murtala Nyako bayan tsigewar da majalisar dokokin jihar ta yi masa.

Wata sanarwa da Hukumar zaben ta fitar na cewa matakin ya biyo bayan umarnin kotu ne da ya hana ta gudanar da wani zaben cike-gurbi a kujerar gwamnan Adamawa.

Kotun ta ce Mataimakin gwamnan Adamawa, Bala Ngilari bai yi murabus ba, don haka rantsar da Ahmed Fintiri a matsayin mukaddashin gwamnan jihar ya saba doka.